Kungiyar kiristoci ta Nijeriya CAN ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da kaunar juna, tana mai jaddada cewa, Nijeriya za ta iya kaiwa ga kololuwar nasara idan ‘yan Nijeriya suka yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakanin su, suka hada kai don gina kasa mai daraja, hadin kai, da dimbin arziki.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a sakonsa na Sallah domin taya al’ummar Musulmin Nijeriya murnar bikin Babbar Sallah (Eid-el-Kabir).
A cewar shugaban kungiyar ta CAN, Hedikwatar kungiyar ta kiristoci ta bi sahun al’ummar musulmi wajen tunawa da kimar sadaukarwa, soyayya, da biyayya da wannan rana ke wakilta.
“Muna sake yi wa ‘yan uwa musulmi barka da Sallah (Eid-el-Kabir) tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da baiwa al’ummarmu zaman lafiya da hadin kai da kuma wadata,” inji shi.