• English
  • Business News
Friday, August 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano

by Sadiq
1 month ago
in Manyan Labarai
0
Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta kama mutane shida tare da rufe wasu shaguna a kasuwar Sabon Gari da ke Kano, saboda sayar da man da ake koɗar da fata ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban hukumar na Jihar Kano, Kasim Ibrahim, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga jama’a ta kafafen sada zumunta, tare da umarnin kai-tsaye daga shugabar hukumar ta ƙasa.

  • Sayar Da Makamai: Goyon Baya Ko Cin Riba?
  • Majalisa Ta Yi Allah-wadai Da Kashe Wasu Matafiya ‘Yan Kaduna 13 A Jihar Filato

“Bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga mutane ta kafafen sada zumunta, muka fara bincike a ɓoye tare da sayen kayan a asirce domin duba sahihancinsu,” in ji Ibrahim.

Ya bayyana cewa binciken ya gano wasu mutane guda shida da ke da hannu wajen rabawa da amfani da waɗannan mayuka ba tare da izini ba.

“Waɗannan kayayyaki sun kasance kamar kayan gyaran fata a wuraren kwalliya, amma suna ɗauke da sinadarai masu haɗari waɗanda ba a amince da su ba,” in ji shi.

Labarai Masu Nasaba

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin

Haɗin gwiwar NAFDAC da sashen bincike da aiwatar da dokokinta ne ya kai ga kama waɗanda ake zargi tare da rufe shagunan da suka shafa, da ɗaukar samfurin mayukan domin gwaji a ɗakin bincike.

Haka kuma, an rufe wasu kamfanonin da ke kwaikwayon kayayyakin da aka yi wa rijista ko suke karya ƙa’idodin NAFDAC, har sai an kammala bincike.

Ibrahim ya roƙi jama’a da su kasance masu lura da duk wani abu da ya saɓa wa doka kuma su riƙa sanar da hukumar nan take.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BilicinKano ShagunaMayukaNAFDACSabon Gari
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sayar Da Makamai: Goyon Baya Ko Cin Riba?

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

Related

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

8 hours ago
Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin
Manyan Labarai

Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin

13 hours ago
Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
Manyan Labarai

Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano

18 hours ago
Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi

20 hours ago
Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
Manyan Labarai

Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II

23 hours ago
Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
Manyan Labarai

Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

2 days ago
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

LABARAI MASU NASABA

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

August 7, 2025
Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

August 7, 2025
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 7, 2025
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

August 7, 2025
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

August 7, 2025
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

August 7, 2025
Neja

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

August 7, 2025
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

August 7, 2025
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

August 7, 2025
Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

August 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.