Kafar CGTN ta kasar Sin, da cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani ta jami’ar Renmin ta kasar Sin, sun yi hadin gwiwar gudanar da binciken jin ra’ayin jama’a, dangane da cikakken zama na 4 na kwamitin kolin JKS na karo na 20.
Cikin sama da shekaru uku a jere, binciken ya tattara ra’ayoyin mutane 47,000 daga kasashen duniya 46. Ya kuma tattara ra’ayoyin mutane daga kasashe masu sukuni, da ma kasashe masu samun saurin ci gaba da masu tasowa.
Sakamakon binciken na shekarar nan ta 2025, ya nuna gamsuwar kaso 89.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi da karfin tattalin arzikin kasar Sin, inda cikin adadin masu bayyana ra’ayoyin ‘yan kasa da shekaru 44 suka jinjinawa karfin tattalin arzikin Sin da sama da kaso 90 bisa dari. Kazalika, kaso 89.3 bisa dari sun jinjinawa kasar Sin bisa yadda ta wanzar da ci gaba bisa matsayin koli. Kana kaso 86.4 bisa dari suka yaba da muhimmiyar gudummawar kasar Sin ga bunkasar tattalin arzikin duniya, ciki har da al’ummun Afirka, da na kudancin Amurka, da Asiya dake kan gaba wajen nuna gamsuwarsu, da kaso 95.6, da kaso 92.9, da 85.6 bisa dari, yayin da ‘yan shekaru kasa da 44 cikinsu suka nuna sama da kaso 88 bisa dari na gamsuwa.
Yayin da yanayin duniya ke fama da fadadar matakan kashin kai da kariyar cinikayya, masu bayyana ra’ayoyin sun bayyana gamsuwa da tabbacin kasuwar kasar Sin, da damammakin da bude kofar kasar bisa matsayin koli ke samarwa duniya.
A shekarar nan ta 2025, binciken ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na kallon kasar Sin a matsayin mai bude kofa, wadda kuma ke amincewa da takara. Har ila yau, kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin na samar da muhimman damammaki ga kasashensu. Kaso 79.8 bisa dari kuma, na kallon Sin a matsayin mai samar da kyakkyawar damar gudanar da kasuwanci dake janyo hankulan masu zuba jari na waje. Sai kuma kaso 78 bisa dari, da suka bayyana cewa kasashensu, na matukar amfana daga cinikayyar kasashensu da Sin. (Saminu Alhassan)