Matakin kasar Amurka na amfani da jiragen yakinta samfurin “B-2 Spirit stealth”, wajen jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa sinadaran nukiliyar kasar Iran, karkashin shirin da aka yiwa lakabi da “Midnight Hammer”, ya kara ta’azzara halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Bayan da a fakaice Amurka ta nuna goyon bayanta ga hare-haren Isra’ila, sai kuma ta shiga kaddamar da hare-hare kai tsaye. Game da hakan, kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta shirya, ta fayyace yadda akasarin masu bayyana ra’ayoyi suka soki lamirin Amurka bisa hare-haren da ta aiwatar kan Iran, tare da sukar manufar kasar ta diflomasiyyar waje mai lakabin “Amurka gaban komai”, wadda a cewarsu ta haifar da mummunar ta’asa marar iyaka a Gabas ta Tsakiya.
- Sin Na Fatan Kwamitin Sulhun MDD Zai Goyi Bayan Kuduri Game Da Halin Da Iran Ke Ciki
- Ƴansanda Sun Gano Ƙarin Bama-Bamai 9 Da Basu Fashe Ba A Kano
Sakamakon jin ra’ayin jama’ar ya nuna cewa, kaso 91 bisa dari na masu bayyana mahangarsu, na ganin yayin da sassan kasa da kasa ke tsaka da kiraye-kirayen sassauta rikicin Isra’ila da Iran, matakin Amurka ya zamo tamkar watsawa wuta fetur, da jefa rikicin cikin wani yanayi da ka iya gagara a warware shi. A daya bangaren kuma, kaso 90 na masu bayyana ra’ayoyin na ganin hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin sarrafa sinadaran nukiliyar kasar Iran, sun yi matukar cin karo da dokokin MDD, da ka’idojin cudanyar kasashen duniya, kana ya keta ’yancin kasar Iran, da tsaro da ikon kare yankunanta.
Kazalika, kaso 77 bisa dari sun jaddada cewa, sarkakiyar yankin Gabas ta Tsakiya, ba za ta iya ba da damar wanzar da zaman lafiya mai dorewa a shiyyar da karfin soji ba, kana za a iya warware batun nukiliyar Iran, da tashe-tashen hankula tsakanin Isra’ila da falasdinawa ne kadai ta hanyoyin siyasa, da tattaunawa da hawa teburin shawarwari.
An gudanar da kuri’un jin ra’ayin ne ta dandalolin CGTN na Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha, inda mutane 10,472 dake kasashen ketare suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp