Wannan fitaccen wasan tatsuniya ta kasar Sin mai suna Wukong ko Black Myth a turance, ta kafa wani sabon tarihi. Wannan wasa, wadda aka yi a kan tarihin kasar Sin, ta zama wasa ta farko da aka fi bugawa a manhajar Steam a cikin sa’a guda da kaddamar da ita, kuma ta samu yabo daga ‘yan wasa na duniya.Â
Bisa wani binciken da kafar CGTN ta gudanar, akasarin masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, wannan wasa na nuna karfin masana’antar wasanni da ake bugawa ta manhaja ta kasar Sin, da kuma kara wa mutane sha’awarsu a kan al’adun gargajiyar kasar Sin.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Sadarwa
- Kasar Sin: Shirin EU Na Kakaba Haraji Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin Ya Sabawa Tarihi
A cikin binciken, kashi 92.1 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa wasan ya samar da wata sabuwar hanya ga ‘yan wasa daga kasashe daban-daban don su fahimci fitattun al’adun gargajiya daga kasar Sin, yayin da kashi 89.6 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyinsu suka ce, suna son su samu karin bayani game da tatsuniyar kasar Sin mai taken Bulaguro Zuwa Yamma ko Journey to the West a turance, yayin da suke nuna sha’awar koyon al’adun gargajiyar kasar Sin.
An fitar da binciken ne a kafar CGTN a harsunan Turanci, Spanisanci, Faransanci, Larabci da Rashanci, inda masu amfani da yanar gizo 8,368 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Yahaya)