Harajin da Amurka ta kakabawa sassan kasa da kasa ya yi matukar illata kimarta a matsayin babbar kasa mai fada a ji. A gabar da gwamnatin Amurka mai ci ke cika kwanaki 100 da kama ragamar mulki, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, matakin Amurkan na cin zali ta hanyar kakaba haraji, ya haifar da karuwar kyamarta a dukkanin sassan duniya.
Cikin kasashe 38 da aka gudanar da kuri’un na jin ra’ayin jama’a, 37 sun nuna goyon baya ga matakan Sin na mayar da martani, hadi da amincewar da sassan kasa da kasa suka yi da goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin kasashen duniya.
Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da aka kada daga watan Fabarairu zuwa Afirilun wannan shekara, sun fitar da ra’ayoyin mutane 15,947 daga kasashe 38. Kaso 74.2 bisa dari na jimillarsu na ganin manufofin kakaba haraji na Amurka za su yi matukar illata ci gaban tattalin arzikin kasashensu, adadin da ya karu da kaso 16.3 bisa dari sama da na watanni 2 da suka gabaci hakan.
Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken matakan kara harajin na Amurka ya karu da sama da kaso 20 bisa dari.
(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp