Birnin Yiwu dake gabashin kasar Sin, da aka fi sani da “katafaren kantin duniya” kuma babban mai samar da manhajojin kasuwanci ta intanet na duniya a kasar Sin, ya kimtsa tsaf wajen kaddamar da sabon zagayen gyare-gyaren cinikayya, da nufin karfafa matsayinsa a fagen cinikayyar duniya.
Majalisar kula da al’amuran kasar Sin ta amince da babban shirin zurfafa cikakkun gyare-gyaren cinikayya na duniya a birnin, dake lardin Zhejiang na kasar Sin, kamar yadda aka bayyana a wata takardar gwamnati da aka fitar ranar Larabar nan.
Shirin dai ya zayyana wani buri da nufin inganta gyare-gyare a Yiwu, ta hanyar kara bude kofa tare da sabbin tsare-tsare irin su sabbin hanyoyin cinikayya da ba da sauto a kasuwa, da daukaka ci gaban kasuwancin shigo da kaya, da inganta ayyukan cikakkun sassa masu nasaba da juna da kuma karfafa ka’idodjin cinikayya ta intanet, kamar yadda takardar ta yi bayani a kai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)