An yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wata ma’aikaciyar jinyar jarirai, Lucy Letby, wadda ita ce ta fi yi wa kananan yara kisan dauki dai-dai a tarihin baya-bayan nan na Birtaniya.
An yanke mata hukunci ne bayan samun ta da laifin kashe jarirai bakwai, da kuma yunkurin kashe karin shida a wani asibitin yara da ke Countess of Chester.
Da gangan, Lucy Letby ta rika yi wa jarirai allura da sauran iska a cikin sirinji, kuma ta rika yi wa wasu dura da karfi, sannan ta bai wa jarirai biyu guba da sinadarin insulin.
Bayan yanke mata wannan hukunci, Lucy Letby ba ta nuna wata alamar nadama ba.
A yazu dai Letby za ta shafe tsawon gaba dayan rayuwarta a tsare, inda ta zama mace ta hudu a Birtaniya da aka taba yankewa irin wannan hukunci, wanda shi ne mafi tsanani da ake yankewa mai laifi.
Alkalin kotun Mai shari’a Goss, ya bayyana laifin da Lucy ta aikata a matsayin “babban abin kyama”.
Ya ce “ta aikata abin da ya saba da tunanin dan’adam mai cikakken hankali, da ya san kimar lura da jarirai, kuma babbar cin amanar wadanda suka yarda da aikin ma’aikatan lafiya ne”.
Alkalin ya bayyana ta a matsayin mara tausayi, wadda ke sanya damuwarta cikin aikinta.
Lauyan da ke kare ta, Ben Myers KC, ya ce “Tun bayan fara shari’ar Lucy ta ki musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa, dangane haka ba shi da wani mataki da zai dauka da zai iya kai wa ga rage tsawon hukuncin da aka yanke mata”.
Harabar kotun ta cika makil da iyayen yaran da ma’aikaciyar jinyar ta halaka wa jarirai, har ma wasu sun yi sharbar hawaye a lokacin da alkalin yake karanta hukuncin da ya yanke wa mai laifin.
An ga wasu daga cikin masu sauraron karar rai a bace lokacin da suka saurari bayanan alkalin.
Wata uwa da ita ma, ta rasa danta ta ce “akwai takaici a ce akwai mutumin da zai iya aikata irin wannan mummunar aika-aika”.
Ita ma wata mahaifiya da aka kashe jaririnta cike da bakin ciki, ta sanar da kotun cewa, “ Game da mutuwar danta, tana ganin lamarin kamar a cikin wani fim din ban tsoro”.
Haka zalika, wata uwa da ke rungume da zomon wasa na yara, ta sanar da kotun cewa “Abin da Lucy Letby ta aikata, mugunta ce da kuma babban abin kunya ne sakaci a matsayinta na malamar jinya da aka bai wa amana”.
Su ma iyayen wata jaririya da aka bayyana sunanta da Baby G, wadda ita ce bakwaini mafi kankanta a cikin dukkan jariran, wacce nauyinta bai fi giram 535, sun fada wa kotun cewa: “Allah ya raya ta” amma sai “ta fada hannun shaidanu”.
Kimanin mutum 70 ne aka taba yankewa irin wannan hukunci na daurin rai-da-rai, inda ake ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar hudu a asibiti. Idan aka yanke irin wannan hukunci, ba a taba sauya shi ba, sai dai bisa wasu dalilai na ba sabon ba.
Sauran matan da aka taba yankewa irin wannan hukunci sakamakon yi wa mutane kisan dauki dai-dai, akwai Rose West da Joanna Dennehy, sai kuma Myra Hindley, wadda tun a wancan lokacin ta riga mu gidan gaskiya.
Jagoran jam’iyyar adawa ta Labour, Keir Starmer, ya yi kira ga gwamnati ta tilasta wa masu laifin da ake yanke wa hukunci su rika fuskantar wadanda aka aikata wa laifi, ganin Letby ta ki bayyana a gaban kotu lokacin da aka yanke mata hukunci.
Ya ce “Ina son ganin an dauki mataki cikin gaggawa a wannan shari’a, saboda iyayen wadanda lamarin ya shafa sun shiga mummunar damuwa.
“Muna neman a samar da sauyi a doka wanda zai tilasta wa masu laifi, su saurari hukuncin da ake yanke musu”, in ji shi.
Shi ma Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya ce gazawa ce da kuma tsoro a ce wadanda aka yanke wa hukunci a cikin kotu, su ki fuskantar iyalan da suka aikata wa laifi.