Biritaniya na biyan Faransawa don ta taimaka wajen sintiri a tashar, kuma yarjejeniyar kolin za ta mayar da hankali ne kan kara yawan albarkatun da aka tura domin gudanar da wannan kan iyaka, tare da samar da kudade na tsawon shekaru.
Sunak ya yaba da cewa yana da mahimmanci alakar da ke tsakanin makwabtan biyu gabanin tattaunawar, inda ake sa ran a taron za su kara nuna goyon baya ga Ukraine da tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik.
- Jami’in Najeriya: Inganta Samun Wadata Tare Zai Samar Da Karin Kuzari Ga Ci Gaban Kasar Sin
- Gwamnatin Sin Ta Ba Da Tallafin Hatsi Ga Saliyo
Macron ya yi maraba da Sunak a fadar Elysee, bayan firaministan ya tafi Paris ta jirgin kasa daga Landan. Kuma da yammacin yau ne ake sa ran gudanar da taron manema labarai.
Wannan dai shi ne taron farko da Birtaniya da Faransa cikin shekaru biyar suka yi zaman tattaunawa, bayan Sunak ya zama firaminista a watan Oktoba, biyo bayan saukar Liz Truss da Boris Johnson.
An tsara tattaunawar ne don samar da wata yarjejeniya da za ta dakile kaura daga Faransa, inda Sunak ya yanke shawarar dakile dubunnan masu neman mafaka da ke tsallaka wa kasar ta tsibirin Channel, yayin da itama Faransa ke neman yadda za a kare kan iyakarta.
Biritaniya na biyan Faransa don ta taimaka wajen gudanar da aikin sintiri a tsibirin, kuma yarjejeniyar da za a tattauna a kai za ta mayar da hankali ne kan kara yawan albarkatun da aka tura domin samar da tsaro wannan kan iyaka, tare da samar da kudaden da za a yi amfani da su na tsawon shekaru.