Gwamnatin Britaniya ta sanar da haramtawa hukumar kula da al’amuran ma’aikatan lafiya da masu ba da kulawa a kasar daukar likitoci da ma’aikatan lafiya aiki daga Nijeriya.
Gwamnatin ta sanar da wannan matakin ne a cikin wani kundin tsarin aikin lafiya da masu ayyukan jinkai cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Intanet.
- An Kama ‘Yansanda Biyar Da Dan Kasuwa A Filato
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Kasar Sin Ba Ita Ce Tushen Saka Wa Kasashen Afirka Tarkon Bashi Ba
A yanzu, Nijeriya ta shiga cikin jerin kasashen da suke fama da rashin wadatattun ma’aikatan lafiya a bisa bayyanan WHO.
A watan Maris ne WHO ta fitar da sunayen kasashe 55 da suke fama da kalubalen wadatattun ma’aikatan lafiya ciki, har da Nijeriya.
Sabo da haka, ya kamata a bai wa kasashen Birtaniya, Nijeriya da sauran kasashen da aka ayyana fifiko wajen inganta bai wa ma’aikatan lafiya horo da kuma al’amuran da suka danganci ba da taimako ta yadda za a hana daukan ma’aikatan lafiya a kasashen waje.
Sakon da kundin ya kunsa shi ne “bisa tsarin dokar WHO” kuma kamar yadda karara dokar ta bayyana cewa za a yi wa dokar tsarin aikin kwaskwarima bayan duk shekaru 10, ya kamata a bai wa wadannan kasashen fifiko wajen bai wa ma’aikatan lafiyarsu horon aiki domin su dada samun kwarewar aiki kana a dakatar da daukan su aiki a kasashen waje.
Cibiyoyin lafiya da kuma cibiyoyin da ke bai wa al’umma kulawa, cibiyoyin daukar ma’aikata da sauran masu alaka da daukar ma’aikatan lafiya masu hadin giwa su kiyaye daukar ma’aikatan lafiya daga wadannan kasashe har sai idan an samu tattaunawa ta fahimta tsakanin gwamnatocin kasashen.
WHO ta rubuta sunayen kasashen da ke da bukatar tallafin da kariyar da jan alli. Har idan an cimma jarjejeniya tsakanin kasar da ta haramta cibiyoyin daukar ma’aikata, ana sanya kasar cikin wannan rukunin kasashen.
Dokar ta kuma ce, har idan ba a rubuta sunan kasar da jan alli ba to yana kasancewa a rukunin masu koren alli. Kasashen da aka yi wa haramcin daukar ma’aikata sune Kenya da Nepal kawai.
Idan za a iya tunawa, wani kudirin dokar haramta bai wa likitoci ‘yan Nijeriya da suka samu horon aikinsu a kasar takadar shaidar kwarewar aiki har sai sun kwashe mafi karancin shekaru biyar suna aiki a kasar, ya yi masarar samun karatu na biyu a majalisar wakilan kasar a ranar Alhamis din da ya gabata.
Manufar dokar ita ce rage yawan likitocin da suke neman barin kasar su fita aiki a kasashen waje kana a inganta ayyukan lafiya a Nijeriya.