Fitaccen malamin addinin Musulunci daga Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa duk ganawar da ya taɓa yi da ƴan bindiga a maɓoyarsu an gudanar da ita ne tare da rakiyar ’yansanda, da jami’an gwamnati na jiha da na ƙananan hukumomi.
Sheikh Gumi ya yi wannan ƙarin bayani ne a ranar Asabar, bayan wata taƙaddama tsakaninsa da lauyan kare hakkin ɗan Adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo, wanda ya buƙaci a bincike shi bisa zargin hulɗa da ’yan ta’adda. Malamin ya ce yana shirin kai ƙarar Omirhobo idan bai janye kalamansa ba, yana mai cewa zargin na iya haddasa rikicin addini.
- An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
- Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Sai dai a martanin da ya wallafa a Facebook, Sheikh Gumi ya ce kalaman lauyan ba batanci ba ne, amma kira ne da nufin a gudanar da bincike, duk da cewa ya nuna takaicinsa cewa lauya kamar Omirhobo ya fitar da irin wannan ra’ayi ba tare da cikakken bincike ba.
Gumi ya jaddada cewa ba ya zuwa wajen ’yan bindiga sai tare da jami’an gwamnati, inda ya bayyana cewa ya gano mafi yawan su na yaƙi ne da al’umma saboda rashin adalci da suka fuskanta, kuma suna amfani da kuɗin fansa wajen ci gaba da rayuwa. Ya ƙara da cewa yawancin su suna da niyyar daina ta’addanci muddin gwamnati za ta tabbatar da tsaronsu da na dabbobinsu.
Malamin ya ce manufarsa ita ce kawo ƙarshen rikicin makiyaya da al’umma cikin lumana, ba wai goyon bayan ta’addanci ba. Yana mai cewa kalamansa sun samo asali ne daga bincike da kuma sha’awar ganin an samu zaman lafiya a Nijeriya.














