Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.
A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye adalci da daidaito a duniya, da kuma kare ka’idar WTO da tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori. Har ila yau, ya ce Amurka ita kadai ta tayar da takkadamar haraji, kuma Sin ba za ta yarda da fuska biyu da Amurka ke nunawa ba ko kadan, balle a keta matsayi da ra’ayin da take dauka ko take adalci da daidaito a duniya, don a kai wa ga matsaya daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp