Biyan basukan Nijeriya a farkon watanni bakwai na wannan shekarar ya karu da kaso 53.63 ko dala miliyan 971.47 zuwa dala biliyan 2.78, wanda ya karu kan dala biliyan 1.81 da aka samu a daidai irin wannan lokacin a shekarar 2023.
Wannan bayanin na kunshe ne ta cikin rahoton biyan kudaden kasa da kasa na mako-mako da aka wallafa a shafin yanar gizo ta Babban Bankin Nijeriya (CBN).
- Matsalolin Tsaro Da Ambaliya: ‘Yan Nijeriya Sun Sayo Abinci Daga Waje Na Tiriliyan 3 – CBN
- Emefiele Ya Yi Amfani Da Wakili Wajen Karbar kwangila Daga CBN – Shaida
Bayanan na CBN ya nuna cewa biyan basukan waje ya karu a watan Mayu da dala miliyan 854.36, yayin da na watan Janairu ya biyo baya da dala miliyan 560.51, sai kuma watan Yuli mai dala miliyan 542.
Biyan basukan waje na sauran watanni da suka hada da Febrairu, Maris, da Afrilu sun tsaya kasa da dala miliyan 300, inda kuma aka samu wata mafi karancin biya wato watan Yunin 2024 da aka biya dala miliyan 50.82.
A cewar ofishin kula da basuka (DMO), bashin da ke makale kan Nijeriya ya kai naira tiriliyan 121.6 zuwa karshen zangon farko na wannan shekarar.
Rahoton DMO na cewa, “Bashin da ake bin Nijeriya ya kai tiriliyan 121.67 (dala biliyan 91.46) zuwa ranar 31 ga watan Maris din 2024. Idan aka kwatanta da na ranar 31 watan Disamban 2023, da ya kai tiriliyan 97.34 (Dala biliyan 108.23). Adadin kudin basukan waje sun kai tiriliyan 65.65 (Dala biliyan 46.29), yayin da kuma basukan cikin gida suka kai naira tiriliyan 56.02 (Dala biliyan 42.12).”
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun karin kudin basukan, daraktan bincike da tsare-tsare a Chapel Hill Denham, Tajudeen Ibrahim, ya misalta yawan karuwan basukan da faduwar darajar naira da ya janyo basukan suka kai har haka.
“Akwai tasirin hulda da kudin kasashen waje wajen biyan basuka, na biyu kuma shi ne ya danganta da yanayin lokacin da ka je neman rancen shi ma yana kara tasiri, Nijeriya ta kara ciwo bashi a ciki da waje. Baya ga hakan, akwai zancen faduwar darajar naira, duk sun yi tasiri a wannan bangaren,” ya shaida.
Tunin dai masana suka yi ta gargadin yawan ciwo basuka na kara jefa kasar nan cikin damuwa da yanayi marar tabbas.