Wasu ‘yan Boko Haram/ISWAP sun kai hari a sansanin Sojoji dake Sabon Gari, kusa da Damboa a jihar Borno, inda suka kashe sojoji, wasu kuma aka nemi su aka rasa. ‘Yan ta’addan sun yi amfani da babura da manyan motocin yaƙi a harin da suka kai ƙarfe 4 na Asuba, ranar Asabar.
Bayan Sojojin sun janye don sake shiri, ƙungiyar haɗin gwuiwar Sojojin da CJTF da ƴan sa-kai sun sake karɓar sansanin bayan musayar wuta mai tsanani da ‘yan ta’addan, lamarin da ya sa suka gudu. Sai dai an samu raunuka da asarar kayayyaki, ciki har da motocin aiki na Sojojin.
- Zulum Ya Ƙaddamar Da Fara Aikin Titin Jirgin Ƙasa A Borno
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 2, Sun Jikkata 3 A Borno
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa akwai haɗin kai tsakanin wasu mazauna yankin Damboa da ‘yan ta’addan, inda suke ba su bayani da kayan abinci don sauƙaƙa musu kai hare-hare. Akwai sauran yankunan jihar Borno da ke fama da irin waɗannan matsaloli kamar Gwoza, Askira-Uba da wasu sassan Biu.
Har yanzu ba a samu wata sanarwa daga hukumomin tsaro ba game da wannan hari a lokacin tattara rahoton nan ba.