AÆ™alla mutane 12 ne ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kashe a Æ™aramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Mai Martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya shaida wa LEADERSHIP cewa ‘yan Æ™ungiyar sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) guda biyu sun rasa ransu a harin kwanton-É“auna a kan hanyar Kirawa a ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilu, 2025.
- Yadda Sakamakon Jawo Jarin Waje A Rubu’in Farko Na Bana Ya Ba Da Sha’awa A Kasar Sin
- Zulum Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Boko Haram Ke Dawowa Wasu Yankuna A Borno
A ranar Asabar, 26 ga watan Afrilu, wasu mutane 10 da suka je yin itacen girki a daji an kashe su a ƙauyen Bokko Ghide.
Wasu biyu kuma sun ji rauni sosai a harin.
Sarkin ya bayyana takaicinsa kan yawaitar hare-hare, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga Æ™oÆ™arin da gwamnatin Jihar Borno da sojoji ke yi na sake gina yankuna da kuma dawo da ‘yan gudun hijira gida.
“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau.
“Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waÉ—anda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin.
Ya yi addu’a Allah ya jiÆ™an mamatan ya kuma bai wa waÉ—anda suka jikkata lafiya.
Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa Æ™oÆ™arinsu amma ya buÆ™aci a Æ™ara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu Æ™arfi domin yaÆ™ar ‘yan ta’addan.
Ya yi gargaÉ—in cewa waÉ—annan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa.
A wani É“angare kuma, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake kira ga rundunar soji da su É—auki mataki wajen fatattakar ‘yan Boko Haram daga maÉ“oyarsu.
Gwamna Zulum ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, da sauran manyan hafsoshin soji a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp