Mutum biyu sun rasa rayukansu, sannan wasu uku sun jikkata yayin da wani ɗan Boko Haram ya kai hari ta hanyar tashin bam a wajen wani taron makokin mutane a Dalori, karamar hukumar Konduga, kusa da Maiduguri, Jihar Borno.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, ɗan ƙunar baƙin waken ya shiga cikin jama’ar da suke makokin mutumin da Boko Haram suka kashe a wani hari, sannan ya tayar da bam ɗin.
Harin na farko da ya faru a ranar Talata, ya kuma jikkata mutum biyu, kuma jama’ar sun taru domin makokin wanda aka kashe.
Kakakin ‘yansandan Jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “An samu rahoton harin bam a Dalori, amma yanzu komai ya koma daidai.”
A wani hari daban, a ranar da ta gabata, mayaƙan ISWAP sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Wajiroko, a ƙaramar hukumar Damboa.
Mayaƙan sun yi amfani da makamai iri-iri wajen kai harin, amma sojojin sun daƙile su da farko.
Sai dai daga bisani ‘yan ta’addan suka dawo da jiragen sama marasa matuƙa ɗauke da bama-bamai.
Sojoji biyar sun jikkata, sannan an lalata wasu kayan aikin sojojin yayin wannan artabu.
Rundunar sojoji ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba tukuna.