‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari Æ™auyen Yamtake da ke Æ™aramar hukumar Gwoza a Jihar Borno da dare ranar Alhamis, inda suka kashe sojoji biyu da wasu mutane da dama.
Harin ya auku ne a sansanin sojoji da ke Æ™auyen kafin ‘yan ta’addan su shiga cikin garin.
- Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
- Dokar-ta-baci: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Gargadi Kantoman Ribas
Wani jami’in soja ya tabbatar da kashe sojojin amma ya ce cikakken bayani zai biyo baya.
Sanata Ali Ndume, ya ce harin abin baƙin ciki ne, musamman ganin cewa gwamnati ta dawo da mazauna garin kwanan nan.
Ya Æ™ara da cewa sojoji sun daÆ™ile wani yunÆ™uri da ‘yan ta’addan suka yi na shiga garin Gwoza bayan harin.
Ndume, ya yaba wa jarumtakar dakarun Nijeriya, amma ya buƙaci ƙarin matakan tsaro.
Ya buƙaci gwamnati ta taimaka wa ƙungiyoyin tsaron al’umma da kayan aiki da makamai na zamani.
Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da ake fama da su a Jihar Borno a cikin ‘yan kwanakin nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp