Wasu ‘yan ta’adda da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun yi garkuwa da wani alkalin babbar kotun ƙasa, mai shari’a Haruna Mshelia, tare da matarsa da direbansa da kuma mai tsaron su a hanyar Damaturu-Kamiya zuwa Buratai-Buni Gari a jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a hanyar Buratai-Buni-Gari a daidai lokacin da mai shari’a Mshelia ke komawa Maiduguri inda yake aiki a babbar kotu a jihar Borno.
- Shehun Borno Ya Bukaci Tinubu Ya Kwato Kananan Hukumomin Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram
- Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno
Wata majiya ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai ne suka tare motar Alkalin tare da tare hanya duk da yunkurin tserewa da ya yi, sai wasu gungun ‘yan tadar sun tare motar ta baya, daga bisani suka tasa ƙeyarsu zuwa dajin Sambisa.
Rundunar ‘yansandan jihar Borno, ta bakin kakakinta, ASP Nahum Daso, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce duk da cewa ba a tuntubi ‘yan ta’addar ba, rundunar ‘yansandan na bin da dukkan matakan tsaro da suka dace domin samun nasarar kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya.
Ana zaton samun wadannan yawaitar sace-sacen ma su muni suna faruwa ne a sakamakon munin hanyar, musamman daga kan iyakar Borno da Yobe zuwa Biu da kuma titin Magza-Kamiya zuwa Buratai, duk kuwa da kasancewar wasu shingayen binciken ababan hawa na sojoji da kuma ‘Rundunar Soji ta musamman’ makarantar horar da sojoji da ke yankin.