Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya tabbatar da cewa ƙungiyar Boko Haram ta taɓa bayyana marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai wakilce ta wajen tattaunawar sulhu a shekara ta 2012, kafin ya zama shugaban ƙasa.
Furucin Dalung, ya sha bambam da na tsohon kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu, wanda ya ƙaryata iƙirarin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yi a taron ƙaddamar da wani littafi a Abuja.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa
- Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewar Dalung, mai magana da yawun Boko Haram a lokacin, Habu Kaka, ne ya bayyana a gidan rediyon Deutsche Welle Hausa cewa sun zaɓi Buhari, Dalung, da malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gerei Argungu don su wakilci ƙungiyar a tattaunawar zaman sulhu da gwamnati.
Sai dai ya ce Buhari bai aminta ya yi musu wakilci ba.
Dalung ya ce maganganun Jonathan suna da nasaba da siyasa, amma gaskiyar lamarin dai ta taɓa faruwa.
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”