Borussia Dortmund ta kori kocinta Nuri Sahin bayan da Bologna ta doke ta a wasan zagaye na 7 na gasar zakarun Turai.
Kungiyar ta Jamus ta yi rashin nasara a wasanni hudu a jere a dukkan gasa tun bayan dawowa daga hutun hunturu.
- Saudiyya Ta Ware Dala Biliyan 100 Don Sabunta Masallatan Harami
- An Sallami Saif Ali Khan Daga Asibiti Bayan Harin Da Aka Kai Masa
Kashin da suka sha a hannun kungiyar ta kasar Italiya da ci 2-1 a ranar Talata, shi ne rashin nasara na uku da suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai na bana, hakan na nufin dole ne Dortmund ta doke Shakhtar Donetsk a wasan karshe na gasar idan ta na son ta kai ga matakin 16 kai tsaye.
Sahin, mai shekaru 36, wanda ya taba taka leda a kulob din a matsayin dan wasa, ya ce “Abin takaici, ba mu yi nasarar cimma burinmu na lashe dukkan wasannin Borussia Dortmund a kakar wasa ta bana ba.
“Ina yi wa wannan kungiya, fatan alheri”.
An nada Sahin kocin Dortmund ne a watan Yunin 2024 a matsayin wanda zai maye gurbin Edin Terzic, wanda ya bar kungiyar bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Real Madrid.