Bisa wasu alƙaluma da Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa da ke aikin jin ƙai wato Red Cross ta fitar a kwanan baya, sun nuna cewa, aƙalla ƴan Nijeriya dubu 23,659 ne suka ɓace, waɗanda kuma har yau, ƴanuwansu ba su sake jin ɗuriyarsu ba. Wannan lamari ke ci gaba da jefa rayuwar ƴanuwa aƙalla dubu 13,595 a cikin fargaba.
A saboda hakan, ake ganin ya zama wajibi matakan gwamnati uku na ƙasar su gaggauta ɗaukar matakan gaggawa domin a lalubo mafita. Red Cross ta fitar da waɗannan alƙaluman ne a yayin zagayowar ranar ɓacewar mutane ta duniya da aka gudanar a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta yi nuni da cewa, batun ya fi ƙarfin alƙaluma, domin irin halin damuwa da iyaye mata da ƴaƴansu ke shiga musamman sakamakon hare-haren ƴan ta’adda.
- ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi
- An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
Kazalika, tafiye-tafiyen ƴan cinari a ciki da wajen ƙasar na ƙara haifar da ɓacewar mutane wanda hakan ya janyo mutuwarsu, ƴanuwansu kuma ba su sake jin ɗuriyarsu ba. Idan da gawar aka gani, hakan na sauƙaƙa wa iyali maimakon a ce sun ɓace gaba ɗaya. Batun kuma ba wai kawai ya tsaya kan waɗanda suka rasa ƴanuwansu ba, hatta al’umma gaba ɗaya na shiga cikin tsoro mai yuwa su fuskanci irin wannan matsala.
Matakan da gwamnati ke ɗauka kan lamarin sun yi ƙaranci. Ko da yake hukumomin tsaro na fitar da sanarwar ceto wasu daga cikin mutanen da suka ɓace, yawan ɓacewar mutane ya sa ya zama wajibi a ɗauki tsare-tsaren da za su magance wannan matsala. Har yanzu babu wani ingantaccen tsari na ƙasa da aka samar domin magance matsalar, balle a ware kuɗaɗe don tallafa wa ƴan uwa da lamarin ya shafa.
Ƴanuwan da ke kai rahoton ɓacewar mutanensu kuma suna fuskantar ɓata lokaci saboda tsararan tsare-tsare, abin da ke hana su samar da bayanan da suka kamata. Sai dai ƙungiyoyi kamar ICRC sun samar da tsarin zamani kan lamarin, wanda ya ba su damar gano wasu da suka ɓace tare da miƙa su ga iyalansu, har ma da tattara sabbin sunaye 451 na waɗanda suka ɓace. Amma bai kamata a bar irin waɗannan ƙungiyoyi kaɗai da nauyin ba, domin abu ne da gwamnati itama ta kamata ta ɗauki nauyi.
Ya kamata a kafa hukumar musamman da za ta kula da gano mutane da suka ɓace tare da bata ƙarfi don gudanar da bincike. Kaso 68 cikin 100 na masu neman ƴaƴan da suka ɓace iyaye mata ne, amma da dama suna dawowa hannu rabbana saboda rashin tsari daga mahukunta. A jihar Yobe kaɗai, yara 2,500 ne aka ce sun ɓace, mafi yawan su a Gujba, abin da ya nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka a Arewa maso Gabas.
Yakuma zama wajibi a samar da tsare-tsaren gwamnati da za su kare haƙƙin ƴanuwa waɗanda suka rasa nasu, musamman a jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula. Waɗannan tsare-tsaren za su yi aiki kaf shoulder da al’ummomin yankuna, sarakunan gargajiya, malaman addini da ƙungiyoyin sa kai.
Haka kuma dole al’umma su tsaya tsayin daka wajen bai wa iyalan waɗanda suka ɓace kariya daga nuna masu ƙyama tare da taimaka musu da tallafin da suke matuƙar buƙata.














