A kwanan baya ne, aka ruwaito, Babban Hafsan Rundunar Tsaro Janar Christopher Musa, ya bayar da shawarar da a katange iyakokin Nijeriya, domin a kara tabbatar da tsaro a kasar.
Za a iya cewa, kiran na sa, ya zo a kan gaba, duba da yadda ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen rashin tsaro, musamman a yankin Arewa ta Gabas da kuma a wasu sasssan ƙasar.
A bayanin na Janar Musa, ya yi nuni da cewa, ƙasashen duniya da dama, sun rungumi wannan salon, na katange iyakokin ƙasarsu, domin daƙile ƙalubalen rashin tsaro.
Hafsan, ya buga misali da ƙasashen Fakistan da Saudi Arabiya, inda Fakistan, ta gina Katanga da iyakar ƙasar Afghanistan, domin daƙile aukuwar rikice-rikice, a tsakanin ƙasashen biyu, inda kuma Saudi Arabiya, ta gina katanta tsakaninta da ƙasar Iraƙ, domin daƙile kutsen masu ra’ayin riƙau na addini zuwa cikin ƙasarta.
- NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”
- Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Da Japan Ta Yi Game Da Kusantar Iyakarta Ta Sama
A nan, wannan Jaridar, ta goyi bayan wannan ra’ayin na Janar Musa, domin kuwa samar da tsaro a iyakoki, musamman a yankin Arewa Maso Gabas, abu ne, da yake da matuƙar mahimmanci.
Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci.
Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa, yadda aka bar iyakokin ƙasar sakakai ne, ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasa, inda wasu’yan ta’adda daga wajen ƙasar, ke yin amfani da damar, wajen shigowa tare da kuma shigo da muggan makamai da yadda masu ra’ayin riƙau na addini, daga ƙasashe kamar su, Mali da Jamhuriyar Nijar da Chadi, ke shigowa ƙasar, su kuma ci Karensu ba babbaka.
Misali, ‘yan ta’addar ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi, waɗanda ta hanyar ayyukan ta’addacin su, suka hana wasu yankuna musamman a Arewa Maso Yamma sakat, daga nan kuma suka ƙara faɗaɗa ta’addacinsu, zuwa wasu yankuna na Arewa Maso Gabas da kuma zuwa iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
Hakazalika, wasu rahotanni sun nuna cewa, ‘yan ta’addar Lakurawan ‘yan aware nada alaka da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da ayyukansu na ta’addanci, a yankin Sahel, waɗanda shigarwarsu wasu yankuna na Arewa Maso Yammacin ƙasar nan, suka samu damar janyo suke janyo ra’ayoyin wasu matasa cikin ƙungiyar da kuma auren wasu da yankunan na Arewa Maso Yamma.
Shi ma wani tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar Majo Janar Edward Buba, ya sanar da cewa, ƙungiyar ce, ta ƙara haifar da rudanin siyasa a ƙasashen Mali da Jamhuriyyar Nijar.
Kamar yadda Janar Musa ya faɗa, katange iyakon Nijeriya abu da ke da alfanu da dama ga ƙasar, musamman domin ci gaba da dorewar ƙasar da kuma kare ta, daga hare-hare daga ketare.
Tabbas batun Katange ƙasar, abu ne, da zai laƙumi ɗimbin kuɗaɗe, amma aiwatar da hakan, zai kare Nijeriya daga kutsen ‘yan ta’adda daga wajen aasar.
A wani rahoto da Asusun da ke tallawa kananan yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF, ya yi gargaɗin cewa, rikice-rikicen da ke aukuwa a yankin Sahel ta tsakiya, na kutsawa zuwa wasu ƙasashen da ke maƙwabtaka na yankin, wanda hakan ke kara ta’azzara tarwatsa alumomi daga yankunan su da haifar da matsin tattalin arziki da kuma haifar da karanci kuɗaɗe.
Duba da yadda iyakokin Nijeriya suke sakakai, wannan matsalar za iya cewa, tamkar kasar, na zaune, a karkashin Bam.
Ya zama wajibi mahukunta a Nijeriya su ɗauki dabaru Nijeriya wajen daƙile shigowar ‘yan ta’adda cikin ƙasar.
Duk da cewar, katange iyakon Nijeriya ba zai hana kutsowar ‘yan ta’adda ba, amma katangewar, za ta taimaka wa hukumomin tsaron ƙasar wajen ƙaukar matakan gaggawa na mayar da martani, ta hanyar yin amfani da kayan aiki na sanya ido.
Tsawon iyakonin Nijeriya, ya kai sama da kilomita 4,000 kilomita, wanda hakan ke nuna cewa, sun fi ƙarfin jami’an hukumar kula da shige da fice, iya kula da iyakokin su kaɗai.
Hakazalika, salon shugabanci a ƙasar na rashin nuna damuwa, ya sanya iyakokin ƙasar sun kasance wajen na samun damar shigowar ɓata gari cikin ƙasar, musamman ga ‘yan ta’addar daga yankin Sahel.
Akwai wasu dabarun zamani da ya kamata a runguma a ƙasa na katange iyakokin ƙasar.
Alamisali, ƙasar Fakistan wadda ta yi iyaka da ƙasar Afghanistan, kusan ta kammala katange iyakokinta masu tsawon kilomita 2,611 wanda aikin ya kai kaso 98.
Kazalika, ƙasar Saudi Arabiya, wadda ta yi iyaka da ƙasar Iraki, ta katange iyakar da ƙasar tsawon kilomita 900 domin daƙile shigowar masu fasakwari da kuma barazanar ‘yan ta’adda.
Wadannan misalan kaɗai, sun isa hujjar da nuna cewa, katange iyakokin ƙasa tare da yin amfani da kayan fasahar zamani, za su taimaka wajen ƙara tabbatar ƙasa.
Batun gaskiya a nan shi ne, mun yi ammanar cewar cewa, rashin tsaron da ke ci gaba da addabar Nijeriya ba daga cikin gida Nijeriya ba ne, daga ƙetare ne.
A ra’ayin wannan Jaridar, muma muna goyon bayan kiran na Janar Musa, na buƙatar a katange iyakokin ƙasa, domin kuwa, bai kamata ace, Nijeriya ta yi wani jinkirin aiwatar da hakan ba. Wannan ne matsayar mu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp