Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce kamfanin ya amince da karin albashin ma’aikata kashi 50 cikin 100.
Rabiu ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda ta cikin gida da shugaban ma’aikata na BUA, Mohammed Wali, ya sanya wa hannu ranar Lahadi a Legas.
- Dalilan Da Suka Sa Har Yanzu Ba A Rage Farashin Simintin BUA Ba
- Bayan Rage Farashin Siminti, BUA Ya Kara Farashin Suga, Fulawa Da Taliya
Sanarwar ta ce, shugaban BUA ya ce karin kudin an yi shi ne don rage radadin matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce karin albashin zai shafi ma’aikata na dindindin/da na wucin-gadi zai kuma fara aiki daga ranar 1 ga Fabrairu, 2024.
“Ana fatan da wannan gagarumin karimcin, zai sa mu kara himma wajen gudanar da ayyukanmu tare da yin iya kokarinmu don tabbatar da irin kwarin guiwar da aka yi mana,” in ji shi.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, sakamakon yanayin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati, kan sabon mafi karancin albashi a kasar.