Kwanan nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton dake sabunta hasashen yanayin tattalin arzikin duniya gami da makomarsa na shekara ta 2025 a tsakiyar shekarar da muke ciki, inda rahoton ke ganin kara harajin kwastam da rashin sanin tabbas game da manufofin cinikayya sun janyo tabarbarewar makomar tattalin arzikin duk duniya, tare da haifar da tarin kalubaloli ga kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin.
Rahoton na hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya na bana, zai ragu zuwa kaso 2.4 bisa dari, yayin da saurin karuwar cinikayya zai ragu zuwa kaso 1.6 bisa dari. Kana, rahoton na ganin cewa, daidaita manufofi gami da hadin-gwiwar kasa da kasa, na da muhimmanci gaya ga samar da ci gaba ga tattalin arzikin duniya, da tabbatar da dorewarsa.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, abubuwa na zahiri sun shaida cewa, dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya muhimmin abu ne da kowa zai amince da shi, kuma bude kofa ga kowa da inganta hadin-gwiwa muhimmin abu ne da ya kamata mu yi a wannan zamanin da muke ciki, kazalika, ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban shi ne zabin da ya zama dole.
Kakakin ya kuma jaddada cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa ga fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma bude kofar kasar Sin, dama ce ga duk duniya har abada. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp