Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba cewa yankin kudancin Kasar Nijeriya ne zai gaji mulkinsa ba a 2023.
Yahaya Bello ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci kan amincewar da kungiyar gwamnonin Arewa suka yi na sauya mulki zuwa yankin kudancin kasar nan, lokacin da ya ke zantawa a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
Gwamnonin Arewa goma sun nuna goyon bayansu na maida shugabancin Kasar Nijeriya Kudancin kasar, suna masu cewa ya dace wani yanki ya karbi ragamar mulki bayan shekaru takwas da Buhari ya yi yana mulki.
Bello, wanda ya ce duk wanda shugaban kasa ya nada a matsayin magajinshi, zai yi biyayya har zuciyarshi, ya ce babu wanda ya sanar da shi wani taron gwamnonin Arewa da ya kai ga yanke wannan shawarar maida mulki kudancin Kasar nan.
Da aka tambaye shi ko shugaba Buhari ya ce za a mayar da shugaban cin kasar nan zuwa yankin Kudu, Bello ya ce, “Ban san inda shugaban kasa ya yi irin wadannan kalaman ba, amma ina so in fada muku asarari cewa idan aka yi la’akari da maganar da ta fito daga masu magana da yawunsa; Cif Adesina da Alhaji Garba Shehu, ba na jin akwai inda shugaban kasa ya yi irin wannan magana.”
Bello ya kara da cewa zai doke dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, idan har ya samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC, yana mai cewa shi kadai ne a cikin masu neman takarar yake da tsari da alkibla.