Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zai bar Nijeriya cikin kwanciyar hankali a lokacin da zai bar mulki a 2023.
Shugaban ya sake ba da wannan tabbacin ne a ranar Larabar a yayin bikin tunawa da sojojin kasar nan na shekarar 2023, wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, a Abuja.
- 2023: Indiya Za Ta Rage Kudin Zuwa Aikin Hajji
- A Dauki Hakikakin Matakai Domin Kyautata Hulda A Tsakanin Sin Da Amurka
Shugaban ya kuma bayyana bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 ga asusun roko, daga nan kuma ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da su ba da hadin kai wajen tallafa wa tsoffin sojojin kasar nan da iyalan wadanda suka mutu, wadanda sadaukarwar da suka yi a baya ya sa kasar nan ta kasance a hade.
Shugaban ya yabawa rundunar sojin kasar nan bisa kokarin da suke yi na ganin kasar nan ta zama wuri mafi aminci ga daukacin ‘yan kasa da maziyartan kasar nan, inda ya ba da tabbacin gwamnatin na ci gaba da ba su tallafi da kuma bukatar tallafin kudi domin ci gaba da kokarinsu.