Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce cike yake da kwarin guiwar lashe zaben 2023 saboda Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ba shi tabbacin gudanar da sahihin zabe.
Atiku, wanda ya yi da jaridar Financial Times (FT) a Landan ya ce, sau biyu su na ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wannan batun.
- Kan ‘Yan Majalisar Jigawa Ya Rabu Kan Batun Tsige Shugaban Karamar HukumaÂ
- Tsare Okupe Ba Zai Hana Ni Zama Shugaban Kasa A 2023 Ba – Peter ObiÂ
“Na samu tabbaci daga shugaban kasa, domin sau biyu muna tattaunawa wannan batun, ya ce ko da wannan shi ne kawai tarihi guda da zai bari, zai tabbatar ya gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci,” in ji Atiku.
A cewarsa, idan ya zama shugaban kasa zai gina wata irin gwamnati wadda za ta hada kan al’ummar Nijeriya kuma zai jawo ‘yan jam’iyyar adawa a jikinsa domin tafiya tare da kowa da kowa.
Da aka tambayi Atiku ko zai yi aiki tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, wanda shi ne abokin takararsa a zaben 2019, Atiku ya amsa da cewa, “me zai hana?’
Da aka sake tambayarsa na cewa wani mukamin zai bai wa Obi, Atiku ya ce “Bari mu fara cin zabe mana kafin a fara tunanin wani rawa mutane za su taka.”
Buhari ya kayar da Atiku a zaben 2019 da kuri’un da basu da yawa sosai, ko da yake Atiku ya yi ikirarin cewa duk da hakan da magudi aka kayar da shi.
Atiku ya kara da cewa, zaben 2023 zai yi matukar wahala a yi magudi duba da cewa an samu ci gaba wajen bijiro da na’urorin zamani wanda hukumar zabe ke shirin amfani da su.