Shugaban Kada Muhammadu Buhari, ya bayyana fadan da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da rundunar masu sanye da kayan sarki ta RSF a Sudan da cewa abin damuwa ne matuka.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da shugaban gwamnatin mulkin soji na kasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Déby ya kai masa ziyara a birnin Makkah da ke Saudiyya a ranar Lahadi.
- Karamar Sallah: Gwamnatin Borno Ta Biya Ma’aikata Albashin Afrilu
- Gobara Ta Tashi A Wani Sashen Kwalejin Queens Da Ke Jihar Legas
Shugaba Buhari ya nuna takaici kan irin asarar rayuka da ake ci gaba da samu sakamakon rikicin.
Shugabannin biyu sun tattauna kan batun rikicin na Sudan, inda suka yi kira ga dukkan kasashe makwabta da kuma al’ummomin waje da su shiga tsakani domin dakatar da fafan.
“Lamarin da ke faruwa a Sudan abin takaici ne. Sudan ta cancanci zaman lafiya idan aka duba halin da ta shiga a baya,” in ji Buhari.
Buhari ya kuma yaba wa shugaban na Chadi kan irin kokari da yake yi na ganin hankali ya kwanta a Sudan da kuma samun zaman lafiya.
Deby-Itno ya fada wa shugaba Buhari cewa abin da ke faruwa a Sudan abin damuwa ne wanda idan ba a dauki matakin shawo kan shi ba, zai iya yin mummunar tasiri kan ƙasashe makwabta.
Shugaban na Chadi ya ce cikin irin matakai da kasarsa ta dauka kan rikicin, sun hada rufe iyakar kasar da Sudan da kara karfafa matakan tsaro.