Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dakatar da kwamishin zabe na Jihar Adamawa, Barista Hudu Ari daga aiki.
Cikin wata sanarwa da INEC ta fitar, ta ce kwamishinan ya fice daga ofishinta har lokacin da aka sake nemansa.
- Buhari Ya Damu Kan Yadda Rikici Ya Barke A Sudan
- Gobara Ta Tashi A Wani Sashen Kwalejin Queens Da Ke Jihar Legas
INEC ta ce daga yanzu sakataren hukumar a jihar ne zai karvu ragamar gudanar da aiki nan take.
Jami’ar hukumar zaɓlven Zainab Aminu, ta ce an dakatar da kwamishin zaben har sai sun kammala bincike, inda daga nan ne za su bayyana matsayarsu kan lamarin.
A ranar Lahadi ne kwamishinan zaben Jihar Adamawa, ya fito ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka karasa a karshen mako, sai dai INEC ta ce matakin da ya dauka haramtacce ne, don haka ba za a yi amfani da shi ba.
Lamarin da ya haifar da rudani a jihar, wanda hakan ta sanya mutane da dama tofa albarkacin bakinsu.