Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna bacin rai tare da gabatar da tambayoyi ga hukumomin tsaro a bude dangane da harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata tare da kashe mutane biyar da jikkata sama da mutum 18.
A wata sanarwar da hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, shugaba Buhari wanda ya samu takaitaccen bayanin harin daga bakin babban sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Mohammad Lamido Belgore, da Kwanturolan hukumar gidan yarin kasa, Haliru Nababa, sun kuma nuna wa shugaban Buhari wuraren da aka tada bama-bamai da kuma dakin adana bayanai da aka kone.
Buhari a karshen dai ya ce dukkanin ‘yan ta’adda guda 63 da suke tsare a gidan yarin sun gudu amma akwai bayanansu domin an wallafa kuma za a iya sake dawo da bayanan.
Buhari dai kamar sauran ‘yan Nijeriya, ya kadu sosai da harin kuma ya yi tambayoyin da yake neman amsarsu.
“Ta yaya ne masu bada kariya a gidan yarin suka kasa dakile harin?
“Fursunoni nawa ake da su a wannan gidan yarin? Mutum nawa za a iya ganowa?
“Jami’an tsaro nawa ke bakin aiki a lokacin? Mutum nawa ne a cikinsu ke dauke da makamai?
“Me ye suka iya tabukawa lokacin da aka kawo harin? Na’urorin CCTV suna aiki?”
Shugaban kasar wanda aka sanar da shi cewa an sake kamo fursunoni 350, yayin da har yanzu sama da 450 aka kasa gano su, ana ta kokarin daukan matakan yadda za a sake kamo su.