Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya isa Jihar Imo domin ziyarar kaddamar da wasu ayyuka guda uku da gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.
Buhari ya isa filin jirgin saman Sam Mbakwe Cargo da misalin karfe 10:46 na safiyar ranar Talata inda dimbin jama’a da suka hada da jami’an gwamnati, ‘yan kallo da masu raye-raye suka tarbe shi.
- Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab Sama Da 100
- Yankin Zanzibar Na Tanzaniya Ya Karrama Tawagar Likitocin Kasar Sin Da Lambar Yabo Saboda Hidmar Da Suka Bayar
Gwamna Uzodimma ne ya tarbi shugaban kasa.
Bayan an gama liyafar, sai ya duba wani jami’in tsaron da tawagar jami’an soji suka dora, daga nan kuma ya shiga wani jirgi zuwa Orlu domin kaddamar da hanyar Owerri zuwa Orlu tare da rakiyar gwamna Uzodimma.
Sai dai, titin Owerri da ke cike da cunkoson jama’a sun kasance babu kowa yayin da mazauna yankin suka zabi yin biyayya ga umarnin zama a gida da haramtacciyar kungiyar IPOB ta kafa.
An bayar da umarnin ne a matsayin hadin kai ga shugaban kungiyar IPOB da ke tsare, Mazi Nnamdi Kanu, wanda zai gurfana a gaban kotu domin amsa tuhumar da ake masa.