Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da bude sabuwar hanyar da gwamnatin tarayya ta kammala wadda ta tashi daga Nguru zuwa Gashua ta wuce Baymari tare da mikata a hannun gwamnatin jihar Yobe a ranar Lahadi.
Da yake jawabi a madadin shugaban Buhari a wajen taron bude hanyar, Ministan Wutar Lantarki, Abubakar D. Aliyu, ya bayyana aikin hanyar a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatin tarayya ta gudanar a fadin kasar nan domin bunkasa harkokin sufuri da tattalin arziki a kasa.
- Uwa Ta Yi Shahada Bayan Karya Dan Bindiga Da Tabarya Wajen Kare Danta
- An Tabbatar Da Yusuf Baba-Ahmed A Matsayin Mataimakin Peter Obi
Ya ce, “Kamar yadda zaku shaida, zamu mika wannan hanya mai tazarar kilomita sama da 55, wadda ta sada garuruwan Nguru-Gashua- Bayamari a jihar Yobe zuwa jihohin Jigawa da Borno.”
“Har wala yau kuma, hanya ce mai matuqar muhimmanci wadda za ta bunqasa harkokin noma da kasuwanci a wannan yankin.”
A nashi vangaren, Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Nijeriya, Babatunde Fashola, wanda Daraktan kula da manyan hanyoyi- Mr Celestine Shuwusu ya wakilta ya bayyana farin-ciki dangane da yadda ma’aikatar ta fara aikin kana ta kammala tare da mika shi cikin nasara.
Bugu da qari kuma, Mista Fashola ya yaba da cikakken hadin kan ma’aikatar kuxi ta tarayya, zauren majisar dokoki ta qasa, musamman shugaban kwamitin ayyuka na majisa bisa goyon bayan da suka bayar wajen kammala aikin.
Haka zalika ya yaba wa ma’aikatansa, yan kwangila tare da yankunan da aka gudanar da aikin hanyar bisa hadin kai da goyon baya.
Da yake jawabi a bukin bude sabuwar hanyar, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana kaddamar da bude hanyar a matsayin muhimmin tarihi ga al’umar jihar sabanin irin yadda cikin shekaru da yawa gwamnatocin baya suka mayar da jihar saniyar ware.
Bugu da kari gwamna Buni ya bayyana muhimmancin shimfida hanyoyi wajen bunkasa tattalin arziki da raya birane da yankunan karkara.
Kazalika, Gwamna Buni ya yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari dangane da namijin kokari wajen dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
A hannu guda kuma Buni ya jinjina wa sashen zartaswa dangane da amincewa da dawo wa da gwamnatin jihar Yobe Naira Biliyan 18 da ta kashe wajen gina hanyoyi mallakain gwamnatin tarayya.