Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgediya janar Dogara Ahmed a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).
Dogara zai karbi aikin ne a hukumance a ranar Litinin 30 ga watan Janairu, 2023 daga hannun Christy Uba, wacce ta rike mukamin na tsawon watanni kusan uku a matsayin mukaddashiyar darakta janar ta hukumar NYSC.
Uba, wacce itace babbar darakta a hukumar, fadar shugaban kasa ta nada ta a matsayin mukaddashiya mai kula da hukumar biyo bayan tsige Birgediya Janar Mohammed Fadah, bisa zargin rashin iya aiki a 2022.
A ranar 22 ga Nuwambar 2022, NYSC ta sanar da daukaka matsayin Christy Uba zuwa matsayin mukaddashiyar hukumar kula da shirin masu yi wa kasa hidima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp