Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da nadin Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein, a matsayin Akanta-Janar ta kasa.
Nadin nata ya biyo bayan samun nasarar cike tsari da ka’idojin zaben wadda za ta hau kujerar.
- Yadda Za A Dakile Kitsa Labarun Kanzon Kurege A Nijeriya -Keyamo
- ‘Yan Adawa Na Ci Gaba Da Kumfar Baki Kan Nasarar Tinubu
Madein za ta amshi ragamar ofishin ne a hannun Mista Sylva Okolieboh, da ya kasance a matsayin Akanta-Janar na rikon kwarya biyo bayan dakatar da Idris Ahmed daga mukamin kan zarge-zargen rashawa da sama da fadi da dukiyar al’umma.
A halin da ake ciki dai Ahmed Idris na karkashin shari’ar da hukumar yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) kan zarge-zargen rashawa.
Shugaban ma’aikata ta Gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, ce ta sanar da nadin na Madein da shugaban kasan ya yi a ranar Juma’a a Abuja.
A wata sanarwar da daraktan yada labarai na ofishin shugaban ma’aikatan, Mohammed Abdullahi Ahmed, ya ce, nadin na Madein ya fara aiki ne nan take daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayun 2023.
“Kuma sabon nadin zai fara aiki ne nan take. Za ta shiga ofis nan da nan,” a cewarsa.