Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada tsohon mataimakinsa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya tabbatar da nadin a wata wasikar nadin da ya aike wa Bashir Ahmad, mai kwanan wata 20 ga Yuli, 2022.
A cikin wasikar da NAN ta gani a ranar Lahadi a Abuja, Boss Mustapha ya ce nadin ya fara aiki ne daga ranar 19 ga Yuli, 2022.
Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa na tsohon mataimakin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai na yanar gizo bisa ga umarnin shugaban kasa inda ya bukaci duk masu rike da mukaman siyasa da ke son tsayawa takara da su yi murabus.