Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, ya yaba wa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kan yadda ya taimake shi lokacin da wasu ke ƙoƙarin ruguza Majalisar Tarayya a lokacin da yake Kakakin Majalisar Wakilai.
A cikin wata sanarwa mai taken “Girmamawa ga Shugaban Ƙasa na Gaskiya,” Gbajabiamila ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi a gare shi.
- Dubun Wasu Mutane 20 Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Kwara Ta Cika
- An Gudanar Da Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin SCO A Tianjin
“Daya daga cikin manyan abubuwan alfahari a rayuwata shi ne sanin Muhammadu Buhari, yin aiki da shi, da kuma kasancewa abokinsa,” in ji shi.
Ya tuna yadda wasu mutane masu ƙarfi suka yi ƙoƙarin rusa Majalisar Tarayya don son rai, amma Buhari ya ƙi barin a yi amfani da ofishinsa don cutar da majalisar.
“A matsayina na Kakakin Majalisar Wakilai, na samu cikakken goyon bayan Shugaba Buhari duk da yunƙurin wasu da ke son amfani da shi don cimma muradun siyasa ta hanyar hana Majalisa aiki,” in ji Gbajabiamila.
Ya ce a lokacin da lamarin ya ƙara tsananta, ya gana da Buhari, wanda ya tabbatar masa da goyon baya.
“Kamar yadda ya yi alƙawari, Buhari ya ƙi yadda da duk wani yunƙuri na lalata majalisa, kuma hakan ya bai wa Majalisar Tarayya ta 9 damar yin aiki cikin kwanciyar hankali da samar da sabbin manufofi domin ci gaban ‘yan Nijeriya. Wannan ma wani ɓangare ne da ya bari,” in ji shi.
Gbajabiamila ya miƙa ta’aziyyarsa ga Aisha Buhari, ‘ya’yansa da kuma dukkannin dangin Buhari.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin aiki don zaman lafiya don ci gaban ƙasa, inda ya ce hakan shi ne mafi girman girmamawa da za a yi wa Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp