Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya taya jam’iyyar APC murnar nasarar lashe zabukan gwamna a jihohin Imo da Kogi.
A wata sanarwa da mai taimaka masa a kafafen yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Litinin ta ce, tsohon shugaban kasar ya godewa mutanen Jihohin Imo da Kogi kan kara tabbatar da amincewarsu ga babbar jam’iyyar siyasar Nijeriya.
- INEC Ta Ayyana Uzodimma Na APC A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Imo
- Da Dumi-dumi: Ododo Na APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Kogi
“Tsohon shugaban kasar ya mika godiya ta musanman ga shugabannin jam’iyyar da ‘ya’yanta kan kokarin da suka yi wajen ganin Sanata Hope Uzodimma ya sake nasara a matsayin Gwamnan jihar Imo a karo na biyu, da kuma Alhaji Usman Ododo a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi.
“Ina yi musu fatan alheri da fatan za su kammala wa’adinsu lafiya,” Cewar Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp