Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna farin cikinsa kan daga darajar Nijeriya a Idon duniya da wata mai dafa abinci, Hilda Bassey Effiong, mai shekaru 27 ta yi na kafa tarihin zama macen da a tarihin duniya ta kwashe tsawon sa’o’i wurin dafa abinci.
Matar ta samu shiga littafin adana sunayen mutanen masu bajinta na ‘Guinness Book of Records’.
- Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Sha’anin Tsaro
- Hukumar Abinci Ta Duniya Ta Ce A Karon Farko Farashin Abinci Ya Tashi
Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar a ranar Litinin, ya yaba wa matashiyar kan kwarewa a fannin dafa abinci.
Shugaban ya gode wa wadanda suka dauki nauyin shirin na dafa abincin da kuma jami’an gwamnati da suka hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, da fitattun jaruman masana’antar kade-kade da fina-finai, da masu sha’awar dafa abinci kan irin goyon bayan da suka bayar da ya kawo daukakar Nijeriya a Idon duniya.