• English
  • Business News
Tuesday, September 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
in Manyan Labarai
0
Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murna yayin da gwamnatin sa ke cika shekaru biyu a mulki, tare da jan hankalin ‘yan Nijeriya da su takaita tsammaninsu daga gwamnati, yana mai cewa, “gyare-gyare ba sa yin tasiri cikin dare daya.”

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya bukaci a ci gaba da goyon bayan gwamnatin APC, yana mai gargadi cewa kada a bar matsin lamba na siyasar cikin gida ya hana aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata.

  • Tinubu Ya Yi Ƙoƙari, Gyaran Nijeriya Aikin Kowa Da Kowa Ne – Buhari
  • Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn

Sanarwar mai taken “Tinubu Ya Samu Yabon Buhari da Shawararsa a bikin cika shekaru biyu” ta bayyana cewa matsalolin da suka hada da talauci da hauhawar farashin kaya—wadanda suka fi shafar talakawa — gwamnati kadai ba za ta iya magance su ba.

Tun daga hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin Tinubu ta kawo manyan sauye-sauye ciki har da:

  • Kawo karshen tallafin man fetur,
  • Daidaita dokar musayar kuɗi (liberalisation of Naira),
  • Biyan bashin COVID-19 na dala biliyan $3.4 gaba ɗaya,

Sai dai hakan ya janyo matsanancin hauhawar farashi da tsadar rayuwa a cikin gida.

Labarai Masu Nasaba

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara

A ranar 23 ga Mayu, 2025, jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a hukumance a matsayin dan takararta guda daya tilo don zaben 2027, duk da fuskantar sauyin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.

Buhari ya jinjina wa kokarin Tinubu wajen rage talauci da hauhawar farashin kayayyaki, yana mai kira ga fannoni masu zaman kansu da daukacin ‘yan ƙasa da su ba da gudunmawarsu.

Ya kammala da cewa: “Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikar shekaru biyu a ofishi. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da tausayi wajen jagoranci. Mu kuma mu rage tsammaninmu daga gwamnati.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 2027APCBuhariTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsoffin Kansiloli Na APC Sama Da Naira Biliyan 16

Next Post

MDD Ta Gudanar Da Bikin Ranar Tunawa Da Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Duniya Ta 2025

Related

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
Manyan Labarai

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

8 hours ago
Zamfara
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara

14 hours ago
Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato

16 hours ago
Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja
Manyan Labarai

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja

18 hours ago
KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
Manyan Labarai

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

20 hours ago
Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Manyan Labarai

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

1 day ago
Next Post
Zaman lafiya

MDD Ta Gudanar Da Bikin Ranar Tunawa Da Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Duniya Ta 2025

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

September 15, 2025
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

September 15, 2025
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

September 15, 2025
Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata

September 15, 2025
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

September 15, 2025
Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa

Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa

September 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

September 15, 2025
Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

September 15, 2025
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”

September 15, 2025
Neja

Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar

September 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.