Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a Jihar Benue, inda aka kashe gomman mutane a unguwar Umogidi da ke Entekpa-Adoka a karamar hukumar Otukpo a jihar.
Buhari ya bukaci a yi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.
- Ko Messi Zai Iya Komawa Barcelona?
- Abin Da Ya Sa Muka Dage Mukabala Da Dakta Idris Bisa Kalamansa A Kan Manzon Allah – Hukumar Shari’a
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Asabar, ya ce shugaban ya yi Allah-wadai da amfani da ta’addanci a matsayin makami a rikice-rikicen kabilanci, inda ya bukaci a gano maharan tare da maganinsu cikin gaggawa.
Ya mika alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, ya kuma umarci jami’an tsaro da su kara sanya ido a kowane fanni da kuma gaggauta duba yanayin tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
“Tunaninmu da addu’o’inmu na tare da iyalan wadanda aka kashe. Al’ummar kasar nan baki daya sun tsaya tsayin daka wajen yakar ta’addanci da miyagun ayyuka,” in ji shugaban.