Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata, matar hamshamin dan kasuwa, mai taimakon jama’a daga Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata.
Shugaban, a cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce za a tuna da marigayiyar bisa tausayawa da taimakon da ta yi marasa galihu.
- Dan Majalisa Ya Bayar Da Tallafi Tare Da Koyar Da Sana’o’i A Zariya
- Wani Matashi Ya Rataye Kansa A Kan Bishiyar Mongoro A Ekiti
“Tana da sha’awar hidimtawa mutane. Ta kasance mai farin jini mai son raba duk abin da take da shi.
“Rayuwarta mai sauki da tausayi ta kasance abin karfafawa ga duk wadanda ke kewaye da ita,” in ji shi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi ayyukanta na alheri, ya kuma bai wa iyalan Dantata ikon jure wannan rashi da suka yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp