Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Ali Chiroma, wanda ya rasu a ranar Talata.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin tsohon shugaba Buhari, Garba Shehu ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya
- Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Tsohon shugaban ya ce marigayin ya bayar da babbar gudunmawa ga tattalin arziki da kuma kungiyar kwadago.
“Ali Chiroma jajirtaccen mutum ne da ya yi hidima sosai ga kungiyar kwadago da kuma tattalin arzikin kasar nan.”
“Muna addu’ar da muka ta’aziyyarmu ga iyalansa, gwamnati, da muma mutanen jihar Borno. Allah ya ba su hakurin rashinsa,” in ji shi.