Babban bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da sabbin takardun kudi a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2022.
CBN ya sanar a ranar 26 ga Oktoba, 2022 cewa, zai sake fitar da sabon fasalin takardun kudi na N200, N500, da N1,000, daga ranar 15 ga Disamba, 2022, yayin da sabbin kudaden da ake da su kuma za a daina aiki dasu a 31 ga Janairu, 2023.
A wani sabon rahoto a ranar Talata, gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, ya shaidawa manema labarai cewa yanzu za a fitar da sabbin takardun kudin ne domin amfanin jama’a a ranar Laraba.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron kwamitin kula da harkokin kudi (MPC).
Emefiele ya kara jaddada cewa, Babban bankin ba zai sauya kudirin sa ba na daina amfani da wasu takardun kudin kasar a lokacin da ya iyakance.