Shugaba Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa Kasar Koriya ta Kudu ranar Lahadi domin halartar wani taron harkokin lafiya na duniya mai taken World Bio Summit, 2022.
Taron wanda Koriya ta Kudu tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka shirya, na kwanaki biyu zai gudana tsakanin ranakun 25 zuwa 26 ga watan Oktoba.
- 2023: APC Ba Jam’iyyar Da Za A Goya Wa Baya Ba Ce, Sun Rusa Nijeriya – Atiku Ya Gargadi ‘Yan NijeriyaÂ
- An Rufe Babban Taron Wakilan Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Na 20
Taken taron na wannan shekara dai shi ne ‘Makomar Rigakafi da Lafiya’
Sanarwar da Fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Asabar, ta ce Nijeriya tare da wasu kasashen Afirka biyar ne za su halarci taron, wanda za a ba da horo kan yadda za a dinga samar da rigakafin cututtuka bisa fasahar mRNA ga Nahiyar Afirka.
Daga cikin wadanda za su yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa Koriya ta Kudu, akwai ministan lafiya Osagie Ehanire, shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye da shugaban hukumar dakile cututtuka masu yaduwa (NCDC), Dakta Ifedayo Adetifa.
Sauran sun hada da wasu gwamnoni, ministoci da kuma wasu manyan mukarraban gwamnati.
Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce, ana sa ran shugaba Buhari zai dawo gida da zarar an kammala taron.