Jami’ar Bayero ta Kano, ta dakatar da jarabawar zangon karatu na farko na shekarar 2022/2023 sakamakon fara yajin aikin NLC a ranar Talata.
Wannan na cikin wata sanarwa da jami’ar ra fitar a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023, mai dauke da sa hannun mukaddashin magatakardar jami’ar, Amina Umar Abdullahi.
- Babu Ranar Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira – CBN
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Gonakin Manoma 20 A Jihar Neja
Mahukuntan jami’ar sun yanke hukuncin ne biyo bayan mara wa NLC da TUC baya da kungiyoyin jami’o’i suka yi na shiga yajin aikin.
“Bayan yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka shiga a fadin kasar nan, da kuma matakin da kungiyoyin jami’o’i suka dauka na shiga yajin aikin, hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ta yanke shawarar dakatar da jarabawar zangon karatu na farko na 2022/ 2023,” in ji sanarwar.
Jami’ar ta bukaci dalibai da su kwantar da hankalinsu tare da jiran karin bayani daga mahukuntan jami’ar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa yajin aikin ya samo asali ne sakamakon dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a garin Owerri na Jihar Imo a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp