• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Dakatar Da Karuwar Hare-hare A Kan Likitoci – Ra’ayinmu

by Sulaiman
3 years ago
likitoci

A halin yanzu ya zama dole asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya su bada sanarwar gargadi ga marasa lafiya da iyalansu ta cewa likitoci da ma’aikatan lafiya na da hakkin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron barazana ko tsoron kai hare-hare a kan su ba a yayin da suke gudanar da ayyukansu na ceto rayuwar al’umma. Tabarbarewar lamarin hare-hare a kan likitoci da jami’an lafiya a kasar nan ya kai ga haka musamman ganin yadda ake fuskantar karancin likitoci kasar nan, inda wasu kasashen duniya ke yi wa likitocinmu tayin kudade masu tsoka tare da yanayin aiki mai dadin gaske.

Sai kuma ga su wadanda suka zabi zama a cikin gida don aikin su na ceto rayuwar al’umma suna fuskantar hare-hare daga marasa lafiya da iyalansu. A ‘yan wattanin nan an samu karuwar hare-haren a kan likitoci daga marasa lafiya da iyalansu da basu gamsu da wani abu da likitocin suka gudanar ba yayin jinyar ‘yanuwan nasu ko kuma suna zargin sakacin Likitocin ne suka yi sanadiyyar rasuwar ‘yanuwan nasu. Daga dukkan alamu hukumomin asibitocin da jami’an tsaro da hukumomin garuruwan da asibitocin suke basu da karfin da za su iya kawo karshen wannan lamarin da yake karuwa a kullum.

Rahoton hari na baya-bayan nan ya faru ne ana ‘yan kwanaki a shiga sabuwar shekarar nan a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara inda wasu iyalan mara lafiya daya mutu suka farmaki daya daga cikin likitocin asibitin abin da ya sa hukumar asibitin ta kwace gawar dan’uwan mutanen. Dalilin da mutane suka bayar na kai ma Likitan harin shi ne wai sakacinsa ne ya kai ga rasuwar danuwan nasu.

Hukumar asibitin ta nemi a tabbatar da hukunta mutanen da suka aikata wannan laifin yayin da kuniyar Likitocin asibitin suka yi yajin aiki na kwana biyar, amma daga dukkan alamu hare-haren na cigaba da aukuwa babu wata alama ta yiwuwar dakatar da shi.

A bayaninsa, shugaban kungiyar likitoci na Jihar Kwara, Dakta Ola Ahmed, ya ce, a halin yanzu ire-iren wannan hari yana faruwa a kusan duk mako a sassan jihar abin da kuma yake zama tashin hankali ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya. A wani rahoto irin wannan lamarin ya faru a watan Fabrairu na shekarar 2022 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Akure ta Jihar Ondo, danuwan wani mara lafiya ne ya yi wa wani Likita dukan kawo wuka.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

A wani lamarin kuma, Shugaban Kungiyar Likitoci reshen Jihar Bauchi, Dakta Adamu Sambo a taron manema labarai da aka yi a watan Yuli na shekarar 2022, ya bayyana yadda aka kai wa wani Likita hari, inda yake cewa, “A ranar 8 ga watan Yuli na shekarar 2022, Dakta Mohammed Sani, wanda babban jami’in asibitin ne a Babban Asibitin garin Misau, a yayin gudanar da aikinsa wani danuwan mara lafiya ya kai masa hari da gatari da nufin kashe shi, ba zamu amince da wannan haukar a aikin mu na ceto rayuwar al’umma ba.”

“Koma menene koken mutane, ya kamata su mika koken ne ga hukumar da ta dace maimakon daukar doka a hannunsu. Wannan mutumin ya shigo ba tare da sanin halin da ake ciki ba ya kama wani likitan ma da baya cikin wadanda suka yi jinyar danuwan nasa ya shiga saransa da gatari har sau hudu.”

Haka kuma a watan Agusta na shekarar data gabata, iyalan wata mara lafiya sun kai wa wani likiitan mata hari inda suka ji masa mummunan ciwo a kansa, kungiyar likitoci na yankin Abuja sun nuna damuwarsu a kan hare-hare a kan likitoci da dukkan ma’aikatan lafiya a yankin dama kasar gaba daya.”
Kungiyar ta bayyana damuwarta musamman a kan sabbin likitoci dama wadanda suka tsufa in aka lura da yadda aka cusa lamarin hare-haren a asibitocinmu a ‘yan shekarun nan.
Wadannan hare-haren kamar yadda suke faruwa a Nijeriya yana nuna irin halin takaicin da al’umma ke ciki ne a Nijeriya a kan haka yakamata a nemo kwararru a bangaren kula da mutane masu fushi don a wannan lokacin kusan duk wanda ka taba zaka ga yana cikin fushi ne.

Tabbas ana fuskantar talauci, ga kuma tashin hankalin da harkokin ‘yanta’adda masu garkuwa da mutane suka dorawa al’umma da kuma halin tashin hankali da jami’an tsaronmu ke jefa mutane a ciki, lamarin yana matukar shafar tunanin al’umma, daga ka taba mutum sai kawai ya fashe maka. Bayan tabbatar da ganin an hukunta masu kai wa likitoci hari ya kamata hukumomin asibitocinmu su samar da yanayin bayar da shawarwari da magungunan warkar da damuwa ba wai kawai ga marasa lafiya ba har ma da iyalansu da masu jinyar marasa lafiyar gaba daya, musamman ganin wasu ‘yanuwan basu iya fuskantar labarin mutuwar ‘yanuwansu, su kuma kyautata mu’amalarsu da iyalan marasa lafiya.

A matsayinmu na gidan jarida muna sane da sakaci da rashin iya aiki na wasu likitoci da ma’aikatan lafiya wanda hakan ya kan kai ga rasa rayuwar marasa lafiyar da suke jinya. Kamar kowanne lokaci kuma ba a kai ga hukunta su, a kan haka muke kira ga mahukuntan asibitoci su samar da kafar da iyalan marasa lafiya za su iya kai koke a kan likitoci da ma’aikatan lafiya a cikin gaggawa a kuma tabbatar da an yi cikakken bincike tare da hukunta wanda aka a samu da laifi, wannan zai matukar taimaka wa tare da kwantar da hankalin iyalan marasa lafiya, rashin wannan ne yake haifar da daukar doka a hannun su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato
Manyan Labarai

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa
Labarai

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi
Manyan Labarai

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Next Post
Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Fatattakar Al’umma Bayan Cikar Wa’adin Disamba

Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Fatattakar Al’umma Bayan Cikar Wa’adin Disamba

LABARAI MASU NASABA

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.