Samar da Cibiyoyin gudanar da bincike a daukacin fadin duniya, domin samar da ci gaba, na da matukar mahimmanci.
Hakan ne ya sanya kasashen ke ware dimbin kudaden a kai akai ga irin wadannan Cibiyoyin domin a ci gaba da gudanar da yin binciken.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Sin Ta Maida Martani Ga Yiwuwar Daukar Matakin Sojan Amurka A Kan Venezuela
Sai dai, abin dubi a nan shi ne, ba wai kawai zuba kudaden domin gudanar da binciken ne ke da matsala ba, amma yadda za a tattala kudaden domin gudanar da binciken shi ne, babban abin da ya wajaba a mayar da hankali akai.
An ruwaito cewa, a kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta amince da a fitar da Naira biliyan 4.2 domin a gudanar da ayyukan yin bincike guda 158.
Wannan binciken, za a gudanar da shi ne, a karkashin Gidauniyar dake tallafawa makarantun dake gaba da sakandare watoTETFund.
Za a zuba kudin a aikin gudanar da binciken na kasa wato NRF na shekarar 2024.
Kazalika, a cikin sanawar da Gidauniyar ta fitar, ta nuna cewa, Gwamnatin ta kuma amince da a bayar da wasu kwangiloli na kafa guraren gudanar da binciken fasahar zamani da kuma guraren gudanar da kasuwanci guda 18.
Gwamantin ta amince da kafa su ne, biyo bayan shawarin da Gidauniyar ta bayar na a kafa su, shiyoyi shida na kasar nan, a karkashin daukin na 2024.
Daga cikin ayyukan da za a yi sun hada da bunkasa rukunin kananan gidaje a yankunan da ke a kasar, habaka samar da takin zamani mai inganci da bunkasa shirin magance Ciyawa a gonakai da bai wa Masara da aka shuka kariya daga harbin cutuka da sauransu.
Sai dai, damuwar wannan Jaridar shi ne, akasarin wadannan binciken ka kawai karewa da wallafa su ne, a Mujallun Makarantu, ba tare da wanzar da binciken, a zahirance ba, musamman domin amfanin ‘yan Nijeriya.
Bugu da kari, bayanan kwana-kwanan na Bankin Duniya sun nuna cewa, ba a wanzar da binciken a aikace, saboda sauye-sayen da ake samu a kasar.
Wannan matsalar za a iya cewa, na faruwa ne, saboda gibin da ake samu a tsakanin gudanar da bincike da tsari da kuma rashin wanzarwa.
A cewar sanarwar, Nijeriya na fuskanar kalubale a wajen wanzar bincike da kuma batun da ya shafi ci gaba, musamman wajen fadada alfanunun da wadannan batutuwan suke da shi, ga habaka tattalin arzikin kasar.
Matukar ba a gudanar da bincike, za a ci gaba da kasance wa a gidan jiya a kasar.
A cewar Hukumar Kula da Kididdiga ta Kasa NBS, a faro gudanar da yin bincike na hadaka ne kan kimmiyar 1970, wato a lokacin da aka kafa Cibiyar Binciken kimiyya da Fasha ta NCST.
Amma bayan Cibiyar ta NCST ta shafe shekaru shida da kafuwa, an ta samun korafe-korafe, kan banbancin batun bunkasa tattalin arzikin kasa.
Daga baya, a 1973, daukacin sassan gudanar da bincike da ke a ma’aikataun Gwamnati, sun koma a matsayin Cibiyoyi masu cin gashin kansu.
Kasar nan na da sama da Cibiyon gudanar da bincike guda 66 wadanda akasarinsu, Gwamnatin Tarayya ce ta kafa su take kuma samar masu da kudade.
Wasu daga cikin wadannan Cibiyoyin na gudanar da kanannan bincike ne, a fannoni kamarsu, Noma da samar da magunguna da sauransu.
Misali, Cibiyar Bincike kan Harkokin Lafiya NIMR, Cibiyar Binciken Magunguna da ci gabansu ta Najeriya, NIPRD, Cibiyar Nazarin Itacen Man Fuskar NIFOR, Cibiyar Ilimin Kimiyya da Bincike ta Kasa NISER.
Wadannan Ciboyoyin ciki har da na Jami’oin kasar da kuma sauran sassan gudanar da bincike da ke a karkashin hukomin Gwamnati, maufarsu shi ne, su kara bunkasa fannin ilomin Boko da habaka dabari tare da kuma yin amfani da sakamakon bincken da aka gudanar domin samar da mafita.
Gidauniyar da ke bayar da tallafin kiwon lafiya ta Grandbille Medical And Laser, ta bayyana cewa, fannin kiwon lafiya na kasar nan na fama da dimbin manyan kalubale ciki har da cutukan da ke harbin bil Adama da sauran cutukan da ba a iya yada su.
Manyan cutukan su ne, zazzabin cizon Sauro, Kanjamau, Tarin Fuka, Amai da Gudawa, mutuwar Jarirai, cutar Daji da sauransu, wadanda kuma suke ci gaba da yaduwa a kasar.
Koda yake dai, Nijeriya na samar da kayan gwajin cutar ta Kanjamau tare da yunkurin samar da magungunan da ke rage radadin cutar, amma abin takaicin, masu gudanar da bincike ba su iya yin wani abin azo a gani ba, a binciken na su.
Akasarin, ana danganta matsalar gudanar da binciken na rashin samar da wadattaun kudade, wanda hakan ya sanya, ba a samun wani sakamako.
Bangaren samar da magungunan gargajiya, fanni ne, na kasuwanci da ke kunshe da miliyoyin dala a daukacin fadin duniya, wanda aka kiyasata cewa, hada-hadar kasuwancin fannin, ta kai ta sama da dala biliyan 100.
Ya kamata a ce, wannan fannin ya janyo hankulan masu gudanar da bincike da ke a kasar, amma muna ganin cewa, hakan na faruwa ne, saboda rashin hada karfi da karfe, a tsakanin Cibiyoyin gudanar da bincike da kuma masana’antar ta sarrafa magungunan na gargajiya da ke a kasar.
Ra’ayin wannan Jaridar shi ne, masu gudanar da bincike na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa tattalin aziki da inganta kiwon lafiya da rage yin dogaro kan kayan kimiyar zamani, da ake shigowa da su cikin kasar.
A nan, zamu iya cewa, ya zama wajbi masu gudanar da bincike a kasar nan da su amfani da basirarsu domin a ciyar da Nijeriya gaba a fanin bincike, musamman domin a samar da makoma mai kyau, domin amfanin daukacin ‘yan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp