Ya kamata jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kwanakin baya a taron nazarin yaki da ta’addanci ya zama matashiya ga al’umma a kan dangantakar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da harkokin ta’addanci a nahiyar Afirka,da kuma yadda suke daukar nauyin ta’addanci a sassan Nijeriya.
A jawabin ya yi nuni da cewa,bai kamata a kawar da kai daga abubuwan da suke faruwa ba, musamman ma ganin lamarin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ba wai abu ne da ya shafi muhalli da tattalin arziki kawi bane, abu ne da a halin yanzu ya shafi tsaron kasa baka daya.An dade ana sa ido masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba na ci gaba da harkokinsu tare da hadin guiwar al’ummar yankin da ake hakar ma’adanan da kuma taimakon wasu bata gari daga cikin sarakuna gargajiya da kuma jami’an tsaro, akwai kuma sa hannun wasu jami’an gwamnati wadanda suka sa kishin kansu a gaba maimakon kishin kasa.
- Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro
- Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Nuna Kin Amincewa Da Kalamai Masu Matukar Hadari Na Jagoran Taiwan
Sakamakon wannan aiki na rashin gaskiya yana da yawan gaske, domin kuwa ana amfani da dukiyar kasa ne wajen kara wutar matsalar tsraon da ta yi sanadiyyar mutuwar al’ummar Nijeriya masu yawa a sassan kasa.
Kididdgar da ke fitowa ta abin da ke faruwa yana tayar da hankula.A rahoton wani kamfanin da ya shahara a fagen samar da bayanan tsaro mai suna ‘Beacon Security and Intelligence Limited’ ya bayyana cewa,akalla mutum 2,583 ne aka kashe an kuma yi garkuwa da mutum 2,164 a zangon farko na wannan shekarar.
Wannan kididdgar tana nuna cewa, ana kashe akalla mutum 28 tare da yin garkuwa da mutum 24 a kullum a cikin wannan lokacin.Wannan ba abin da za a amince da shi ba ne ya kuma kamata a gagguta daukar matakai masu muhimmanci don kawo karshen wannan bala’in.Amma kuma abubuwan da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ke haifarwa ya wuce matsalar tsaro gaba daya.Bayan barnar da lamarin ke haifarwa ga muhalli, ga kuma cutar da al’ummar yankin da ake hakar ma’adinan,haka kuma lafiyar su na cikin hadari.
Idan za mu iya tunawa a Jihar Zamfara kananan yara 400 suka rasa rayukansu sakamakon gubar dalma da suka shaka a wuraren da ake haka ma’adanin gwal, lamarin ya faru ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013.Kamar dai abin da ke faruwa a yankin Neja Delta inda sakamako hakar man fetur aka illata muhalli ta yadda harkokin rayuwar al’umma a yankin ya shiga matsala.
A ra’ayin wannan jaridar, ya kamata gwamnati ta dauki mataki mai muhimmanci don maganin irin wannan matsalar a sassan kasar nan musamman wuraren da ake hakar ma’adinai. Matakin farko shi ne tabbatar da ana aiki da dokokin da ake da su a kasa game da yadda ake hakar ma’adinai ba tare da cutar da al’umma ba,a kuma sanya al’ummar yankin cikin dukkan tsarin da za a yi domin samun nasarar da ake bukata.
An dade da yin watsi da wadannan dokoki,an bar masu hakar ma’adinai suna cin karensu babu babbaka,babu mai sa ido a kan irin kayan aikin da suke amfani da su wajen aikin hakar ma’adanai da kuma ma’aikatan da suke amfani wajen wannan aikin.
Bugu da kari kuma muna bayar da shawarar cewa, dukkan masu lasisin Bugu kari cikakken kwarewar da ta kamata tare da cikakken shirin kare al’umma da muhalli daga dukkan cutar da aikin hakar ma’adinan zata iya haifarwa ga muhalli.
Ya kuma kamata gwamnatin tarayya da samar da wani tsari da zai tattauna da kamfanoni masu hakar ma’adanai don samar da yarjejeniyar da za ta kare dukkan masu ruwa da tsaki a yankin da ake hakar ma’adinan, kamar Sarakuna gargajiya,da kungiyoyin matasa masu fafutuka, a kuma tabbatar da an bi dukkan dokokin kasa tare da kare hakkin bil adam ba.
Samar da hukumar kula da yankunan hakar ma’adanai kamar dai yadda ake da hukumar kula da yankin Neja Delta, hakan zai iya taimaka wajen daidaita al’amura da bunkasa tattalin arzikn yankin da ake hakar ma’adinai gaba daya.
Akwai kuma bukatar tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsakanin kamfanonin hakara ma’adanai a kasar nan.A tabbatar da ana fitar da kididdiga na gaskiya na abin da ake hakowa da sauran kididdigar yadda ake gudanar da harkoki a bangaren.Yin haka zai taimaka wajen gudanar da harkokin gwamnati cikin gaskiya ta yadda dukkan masu ruwa da tsaki za su amfana da albarkatun da ake samu a yankin gaba daya.
Domin cimma nasarar da ake bukata,ya kamata gwamnati ta tabbatar da ana tafiya tare da al’ummar da ke yankin da ake hakar ma’adanan domin suma su san ana tafiya tare da su musamman ganin yankin da suka dogara da shi ne aka lalata domin a hako ma’adinai an kuma lalata hanyoyin samun abincin su.
A ra’ayinmu kuma ya kamata al’ummar Nijeriya su rungumi kiran da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi na neman hadin kan al’umma domin samun nasarar sake fasalin bangaren ma’adinai ta yadda za a amfana da dukkan abin da zai fito daga sashen ta yadda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.