• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Magance Abubuwan Batsa A Littattafan Makarantun ‘Ya’yanmu

by Leadership Hausa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

A makarantu kamar dai yadda abin yake a wurare da dama, kasar nan na fuskantar matsalolin da suka shafi tabarbarewar tarbiyya, kamar sace-sace, magudin jarabawa, rashin mutunta malamai da hukumomin makaranta zinace-zinace da shaye-shayen miyagun kwayoyi, amma yayin da kasar take ci gaba da neman yadda za ta yi da irin wadanna halayen sai ga shi an fito ta bayan gida da wasu al’aumran da za su ci gaba da rusa mana tarbiyar ‘ya’yanmu.

In ba haka ba, ta yaya za mu bayyana daliliin sanya abubuwan batsa dana ‘yan luwadi a littatafan karatu na ‘yan makarantar Firamare da na sakandari? A kwana-kwanan nan ne kungiyar dalibai musulmi ta kasa MSSN ta nuna damuwarta a kan yadda aka cusa abubuwan da suka shafi jima’i da sauran karatun da suka shafi basta a cikin littatafan karatu na ‘yan makarantar firamare da sakandire a kasar nan.

  • Cire Tallafin Mai: Farashin Kayayyaki Ya Karu Da Kashi 22.41
  • Sin: Bai Kamata A Shigar Da Salon Fito-na-fito Cikin Tsarin Ayyukan Hukumomin Hada-hadar Kudi Na Kasa Da Kasa Ba

Ganin irin wannan katobarar, dole mutum ya yi tambayar menene ya hada darussan Lissafi, Turanci, da sauran durussa da irin hotunan batsa da aka yi amfanim da su a cikin littafan makarantun ‘yan sakandire da firamare a Nijreriya. Wannan na nuna shiri ne na gurbata halayar yara ‘yan makaranta, to da wani dalili?.

A daya daga cikin littafan lissafi na ‘yan makarantar firamare an ba da misali da “kwaroron roba 20 + kwaroron roba 5 – kwaroron roba 2 =ya kama”. Abin tashin hankalin shi ne irin wadannan littatafan da ake amfani da su suna koya wa yara ne yadda za su karfafa zubar da ciki, nadigo, luwadi, amfani da kwaroron roba da kuma hanyar da za su yi amfani da kwaroron roban wajen yin jima’i, wanda haka ke nuna kokari ne nasu na sa yara a hanyar fuskantar abin da ya shafi jima’i tun suna kanana yara.

Wannan abin tashin hankali ne, musamman ma ganin cikin darussan da ake koyarwa sun hada da daukar ciki a kananan shekaru, irin zubar da cikin da yara ‘yan mata za suyi cikin sauki, koya wa yara wasu kalmomi na batsa da hanyoyin da za su kaucewa daukar ciki ta hanyar amfani da magungunan hana daukar ciki da kuma yadda za su ji dadin jima’i ba tare da sun dauki ciki ba, abin mamaki wai dukkan wadannan an amince da sanya su a littafan makarantun firamari da sakandire.

Abin tashin hankalin a nan shi ne yadda ake bayyana wa dalla-dalla yadda ake yin jima’i a cikin littatafan ana karfafa wa yara bukatar su rika mu’amala da masu fama da cutar kanjamau ta hanyar sumbata, karfafa zubar da ciki da kuma karfafa wa yara yin jima’i mai tsafta ta hanyar amfani da kwaroron roba, wadannan na daga cikin abubuwwan da ke a cikin littatafan.

A ra’ayin wannan jaridar, samar da abubuwan batsa a littatafai daidai ya ke da samar da su a fayafauyan bidiyo, babu dalilin da za a samar da littatafan karatu ya zama kuma sanya abubuwan batsa don yin haka zai gurbata hankulan yaran ya kuma haifar da yara mara tarbiya a cikin al’umma.

Amma a nan tambayoyin da ke a bakin yawancin al’ummar Nijeriya shi ne wai suwa suka jagoranci sanya irin wanna abubuwan a cikin littatafan makarantar yaranmu?

A kwanakin baya ne shugaban hukumar makaratun firamare UBE, Farfesa Hamid Bobboi, ya nuna damuwarsa a akan yadda aka samu tabarbarewar tarbiya a makarantunmu, ya dora laifin a kan yadda al’amarin tarbiya ya tabarbare a cikin al’umma.

“Abin tashin hankalin shi ne yadda dukkan gurbataccen tarbiya da ake samu a cikin al’umma ana samunsa a makarantumu musaman makarantan firamare,” in ji Farfesa.

Shugaban na UBEC ya lura cewa, hukumar ta gudanar da bincike a kan tabarbarewar tarbiya a tsakanin makarantunmu, an yi kokarin gano dalili da sakamakon gurbacewar tarbiya a tsakanin makaratunmu. A kan haka UBEC ta gano cewa akwai bukatar sake duba littatafan da ake amfain da su a makarantumu domin tsaftace su daga dukkan abubuwan batsa masu lalata tarbiyar yaranmu. Wannan kuma na nuna bukatar cewa ya kamata a samu masu nunawa UBEC halin da ake ciki na rashin tarbbiya a makarantunmu, musamman bukatan a duba irin littattafan da ake amfani da su a makarantun wanda hastari ne ga tariyar yaranmu.

Kamar yawancin ‘yan Nijeriya amfani da abubuwan batsa a littattafai makarantun mu tamkar wata barazana ce ga tarbiyar yaranmu a cikin al’ummar da Musulmi da Kiristoci suka fi yawa wanda kuma a bayyana yake cewa, addininmu ya haramta wadanna abubuwan.

Tambaya a nan shi ne wai shin hukumomin kula da buga littatafan da ake amfani da su a makarantun basu duba tare da amcewa da wadannan littattafan kuwa?, babu makawa dole wadannan hukumomin su amsa tambayoyin iyaye musamman iyayen da yaransu suka tabu sakamakon wadannan littatafan.

Bayan haka a akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu su gaggauta janye littattafan daga makarantu a daina amfani da su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Litattafan BatsaMakarantu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji

Next Post

Abba Gida-Gida Ya Dakatar Da Shugaban Kwalejin Lafiya Da Na Makarantun Sakandire Na Kano

Related

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
Manyan Labarai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

25 minutes ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

9 hours ago
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma
Da ɗumi-ɗuminsa

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

13 hours ago
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

13 hours ago
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra

16 hours ago
APC: Na Bar PDP Ne Domin Ci Gaba Da Amfana Da Ribar Ofishi Na – Kakakin Majalisar Edo
Manyan Labarai

APC: Na Bar PDP Ne Domin Ci Gaba Da Amfana Da Ribar Ofishi Na – Kakakin Majalisar Edo

2 days ago
Next Post
Miliyan

Abba Gida-Gida Ya Dakatar Da Shugaban Kwalejin Lafiya Da Na Makarantun Sakandire Na Kano

LABARAI MASU NASABA

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

May 9, 2025
Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

May 8, 2025
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

May 8, 2025
Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

May 8, 2025
Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

May 8, 2025
Waiwaye Game Da Gudummawar Shawarar BRI Ga Duniya

Waiwaye Game Da Gudummawar Shawarar BRI Ga Duniya

May 8, 2025
Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?

May 8, 2025
Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki

Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki

May 8, 2025
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

May 8, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

May 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.