Farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 22.41 a watan Mayun 2023, daga kashi 22.22 a watan Afrilun 2023.
Wannan dai ya zuwa ne bisa bayanan hauhawar farashin kayayyaki a watan Mayu da ke kunshe a cikin sabon rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a ranar Alhamis.
- Gwamnan Gombe Ya Nada Njodi Sakataren Gwamnati, Misilli Daraktan Yada Labarai
- ‘Yansanda Sun Sake Kama Wani Tserarren Gidan Yarin Kuje A Jihar Nasarawa
CPI tana auna kimar farashin kayayyaki da ayyuka.
Rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a watan Mayun 2023 ya nuna karuwar maki 0.19% idan aka kwatanta da farashin farashin a watan Afrilun 2023.
“Haka zalika, a kowace shekara, hauhawar farashin na kai maki 4.70% sama da adadin da aka samu a watan Mayu 2022, wanda shi ne (17.71%).
“Wannan ya nuna cewa hauhawar farashin ayayyaki (shekara-shekara) ya karu a cikin watan Mayu 2023 idan aka kwatanta da wannan watan na shekarar da ta gabata.”
Wannan na nufin cewa a cikin watan Mayu 202, matakin gaba daya ya kai 0.03% sama da watan Afrilu 2023, a cewar NBS.
Rahoton ya kuma bayyana cewa canjin kaso a matsakaicin CPI na watanni goma sha biyun da suka gabata ya kai kashi 21.20%, wanda ke nuna karuwar kashi 4.75% idan aka kwatanta da 16.45% da aka samu a watan Mayun 2022.